A yau Lahadi, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, ya ce Sin ta damu da harin bindiga da aka kaiwa tsohon shugaban kasar Amurka Donald Trump, kuma shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya jajantawa tsohon shugaban na Amurka.
Trump ya samu rauni yayin da wani dan bindiga ya harbe shi a birnin Butler na jihar Pennsylvania a jiya Asabar, lokacin da yake yi wa magoya bayansa jawabi. (Saminu Alhassan)
Talla