Da karfe 7 na almurun gobe Lahadi 31 ga watan Disamban nan ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, zai gabatar da jawabin maraba da zuwan sabuwar shekarar 2024.
Za a watsa jawabin na shugaba Xi, wanda zai gabatar a birnin Beijing ta manyan kafofin talabijin da rediyo dake karkashin rukunin CMG, da kuma shafukan yanar gizo da sabbin kafofin yada labarai na zamani, wadanda ke karkashin manyan kafofin watsa labarai na kasar. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp