A gobe Juma’a ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, zai halarci bikin bude gasar wasannin motsa jiki ta daliban jami’o’in kasa da kasa karo na 31, wanda za a kaddamar a birnin Chengdu, fadar mulkin lardin Sichuan, na kudu maso yammacin kasar Sin. Shugaban na Sin zai kuma ayyana bude gasar.
Tuni dai babban gidan rediyo da talabijin na kasar Sin CMG, ya shirya watsa bikin kai tsaye, yayin da kuma kafar yanar gizo ta Xinhuanet, za ta gabatar da bikin kai tsaye ta hanyar hotuna da rubutattun bayanai.
Bugu da kari, a yau Alhamis ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da takwaransa na Indonesia Joko Widodo a birnin Chengdu, fadar mulkin lardin Sichuan dake kudu maso yammacin kasar Sin.
Yayin ganawar tasu, shugaba Xi ya ce yayin da ake bin tafarkin zamanantarwa, da farfado da kasa, Sin da Indonesia suna da manyan moriya masu kama da juna, suna kuma da damammakin bai daya na samun ci gaba, kana abokan tafiya ne na amana.
Ya ce Sin a shirye take, ta zurfafa hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare tare da Indonesia, kana za ta samar da misali na kasashe masu tasowa dake marawa juna baya, wajen cimma moriyar bai daya, da ci gaban juna, ta yadda za a ingiza tabbaci, da karsashin bunkasa yankinsu da ma duniya baki daya.
A nasa bangare kuwa, shugaba Joko, cewa ya yi kasarsa na nacewa manufar nan ta Sin daya tak da duniya, kuma tana da burin ci gaba da karfafa hadin gwiwa tare da Sin a fannin zuba jari, da harkokin kamun kifi a teku, da samar da isasshen abinci, da raya fannin kiwon lafiya, da na hidimomin kula da lafiya, ta yadda za a kara bunkasa ci gaban cikakkiyar dangantakar hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare tsakanin sassan biyu. (Saminu Alhassan)