Yau ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci wani biki a birnin Nur-Sultan, ya kuma karbi lambar yabo ta “Golden Eagle Medal” da shugaban kasar Kazakhstan Kassym-Jomart Tokayev ya ba shi.
Lambar yabo ta “Golden Eagle Medal” ita ce babbar lambar karramawa ta kasar Kazakhstan, da nufin karrama fitattun mutanen da suka ba da gagarumar gudummawa ga gina kasar Kazakhstan, ciki har da shugabannin kasashen waje da suka cimma sakamako mai gamsarwa wajen inganta dangantakar abokantaka ta Kazakhstan da kasashen ketare. (Mai fassarawa: Ibrahim daga CMG Hausa)