Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari, ya taya shugaba Xi Jinping na kasar Sin, murnar sake zabensa da aka yi a matsayin shugaban kasar a wa’adi na 3 na shekaru 5, haka kuma shugaban rundunar sojin jamhuriyar kama’ar kasar Sin.
Wannan na kunshe ne cikin sanarwar da mashawarcinsa na musammam kan harkokin yada labarai Femi Adeshina ya fitar.
A cewar shugaba Buhari, Sin da Nijeriya sun kulla huldar diflomasiyya ne a shekarar 1971. Kuma a shekarun baya-bayan nan, karkashin shugabancin Xi Jinping, dangantakar cinikayya da hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu, sun samu saurin ci gaba. Ya ce ya yi ammana cewa, dangantaka tsakanin kasashen biyu za ta ci gaba da samun nasarori a fannonin siyasa da aikin soja da cinikayya da harkokin kudi da man fetur da iskar gas. Haka ma hadin gwiwa a fannonin sadarwa da aikin gona da ababen more rayuwa da samar da kayayyaki, za su ci gaba da yin zurfi.
Shugaban na Nijeriya ya kuma yi wa gwamnati da al’ummar Sinawa fatan ci gaba da more zaman lafiya da ci gaba, karkashin shugabanci na gari na Xi Jinping. (Mai fassarawa: Fa’iza Mustapha)