An zabi shugaban Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa ta Nijeriya (NPA), Abubakar Dantsoho, Mataimakin Shugaban Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Duniya (IAPH), wanda ya kara tabbatar da karuwar tasirin Nijeriya a harkokin tekun duniya.
Zaben da aka gudanar a birnin Tokyo na kasar Japan, ya sake zama wani muhimmiyar nasara da ci gaba ga Dantsoho, wanda a baya ya kafa tarihi a matsayin dan Nijeriya na farko da ya jagoranci kungiyar kula da tashar jiragen ruwa ta yammacin Afirka da tsakiyar Afirka tun bayan kafuwarta a shekarar 1972.
- AC Milan Ta Amince Da Biyan Yuro Miliyan 36 Domin Daukar Nkunku Daga Chelsea
- Yawan Kayayyakin Da Sin Ta Shigo Da Su Daga Kasashe Masu Karancin Ci Gaba Na Afrika Ya Karu Da Kaso 10.2 Cikin Watanni 7 Da Suka Gabata
Da yake tabbatar da nasarar a cikin wata sanarwa a ranar Talata, mai magana da yawun NPA, Ikechukwu Onyemekara, ya ce, zaben na Dantsoho na nuni da amincewar da duniya ta yi masa na sake raya harkoki a fannin tashoshin ruwan Nijeriya. Shi ma Sakatare-Janar na IAPH, Masahiko Furuichi ya yi maraba da wannan zaben, yana mai cewa, “Ina farin cikin yin aiki tare da ku a cikin IAPH na shekaru masu zuwa.”
An kafa ta a cikin 1955 kuma tana da hedikwata a Tokyo, IAPH kungiya ce ta duniya mai dauke da tashoshin jiragen ruwa fiye da 190, kuma tana gudanar da kasuwanci a cikin ƙasashe 89.
Mambobin kungiyar IAPH suna kula da sama da kashi 60 cikin 100 na cinikin teku da kwantena na duniya. Kungiyar tana taka muhimmiyar rawa wajen tsara manufofin tekun duniya, tare da yin aiki kafada da kafada da Hukumar Kula da Teku ta Duniya, Hukumar Kwastam ta Duniya, da tsarin Majalisar Dinkin Duniya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp