Shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama’ar kasar Sin wato NPC Zhao Leji, ya ce kasar sa a shirye take ta fadada hadin gwiwa na zahiri da kasar Senegal. Kuma za ta ci gaba da tallafawa wanzuwar zaman lafiya da ci gaban nahiyar Afirka, bisa burin ta na taimakawa nahiyar yadda ya kamata.
Zhao Leji, ya bayyana hakan ne yayin tattaunawar sa da shugaban kasar Senegal Macky Sall, a wani bangare na ziyarar aiki da ya yi a Senegal, bisa gayyatar da shugaban majalissar dokokin kasar Amadou Mame Diop ya yi masa.
A nasa bangare kuwa, shugaba Macky Sall cewa ya yi, dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka na FOCAC, ya taka muhimmiyar rawar gani, a fannin karfafa zumunta, da hadin gwiwa tsakanin Afirka da Sin. (Mai fassarawa: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp