A kwanakin baya ne, shugaban kasar Rwanda Paul Kagami, ya bayyana yayin wata zantawa ta musamman da wakilin CMG cewa, yayin da ake inganta shirin raya kasar Rwanda na tsawon shekaru 20 daga shekarar 2000 zuwa 2020, kasar Sin ta taimaka matuka a fannonin zamanintar da abubuwan more rayuwa, da kiwon lafiya da ilimi da sauransu.
Muna godiya matuka ga kasar Sin. Kasar Rwanda za ta kara mayar da hankali wajen samar da ci gaba mai dorewa nan da shekaru 30 dake tafe, muna kuma fatan za mu ci gaba da hadin kai a wannan fanni.
Ya bayyana cewa, nan ba da dadewa ba, za a gudanar da babban taron wakilan JKS karo na 20, taron dake zama wani babban lamari ga kasar Sin.
Muna sa ran haka, bayan wannan babban taro dake tafe, alakar abokantaka dake tsakanin kasashenmu za ta bunkasa zuwa babban matsayi. (Mai fassarawa: Ibrahim daga CMG Hausa)