Wani shugaban makaranta daga jihar Zamfara ya zo na ɗaya a duk faɗin ƙasar nan a wajen bikin karrama Malamai na Shugaban ƙasa na shekarar 2024.
Ranar 5 ga watan Oktobar kowace shekara, rana ce da Ƙungiyar UNESCO ta ware don bikin ranar Malamai ta Duniya, wacce aka fara a shekarar 1994, ranar da aka ware don nuna jinjina, yabo da kuma nuna muhimmanci Malamai wajen ƙara kyautata rayuwar al’umma.
- Gwamnatin Katsina Ta Sha Alwashin Kare Iyakokin Burtali A Jihar
- Yadda Rayuwa Take A Sansanin ‘Yan Gudun Hijira A Nijeriya
Sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume ne ya miƙa kyautar karramawar ta bana, a wani bikin da ya gudana a filin wasa na Eagle Square da ke Abuja.
Shugaban makarantar gwamnati ta Sambo Secondary School da ke Gusau ne ya zama zakara a duk faɗin ƙasar nan a rukunin manyan makarantun gwamnati na ƙasa, inda ya lashe kyautar ta shugaban ƙasa.
An gwangwanje wannan Shugaban makaranta, Mallam Musa Yahaya Paila da wata dalleliyar mota da kuma lambar yabo.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar Zamfara, Sulaiman Bala Idris ya fitar yau a Gusau, ya bayyana cewa wannan mataki na yin nuni da cewa dokar ta-ɓacin da aka sanya wa harkar ilimi a Zamfara a ranar 14 ga watan Satumbar 2023 ya haifar ɗa mai ido.
Gwamnatin Dauda Lawal na cika alƙawarin ta na yi wa harkar ilimi garambawul, wanda gwamnatin ta tarar yana gab sa rushewa.”
Gwamnatin Nijeriya ta gabatar da bikin Malamai na duniya na bana 2024, mai taken “Muhimmantar da Muryoyin Malamai: Hanyar zuwa sabon yanayi ga harkar ilimi.”
A bikin, an karrama Malamai da shugabannin makarantu, tare da ba da kyaututtuka na musamman.
An zaƙulo waɗanda suka amfana ɗin ne daga makaramtun Sakandare da Firamare na gwamnati a duk faɗin ƙasar nan, da kuma makarantu masu zaman kan su, inda suka samu kyaututtukan da suka haɗa da motoci, babura, jannaretoci da sauran su.”