Shugaban Kasar Sin, Xi Jinping ya kafa tarihi a matsayin Shugaban Sin wanda ya samu nasarar yin tazarce zuwa wa’adi na uku a kan mulkin kasar.
Shugaba Xi Jinping ya zama shugaba mafi iko da darajar fada-a-ji bayan tsohon shugaban kasar, Mao Zedong.
A halin yanzu dai Jam’iyyar Kwaminisanci ta Kasar ta tabbatar da Xi a matsayin babban sakataren jam’iyyar wanda hakan ke nuni da cewa, nan da watan Maris mai zuwa, Shugaba Xi yana da tabbacin dorawa a kan mulkin Kasar na wasu shekaru biyar.
Kafin a kawo wannan matakin, tuni manyan kusoshin jam’iyyar suka bayyana goyon bayansu ga tsawaita wa’adin mulkin Shugaba Xi, baya ga amincewa da suka yi ga wasu sauye-sauye masu yawa da suka tilasta wa wasu manyan jami’ai ajiye mukamansu.