Daga ranar 21 zuwa 26 ga watan Satumba ne, shugaban kasar Syria Bashar al-Assad ya halarci bikin bude gasar wasannin motsa jiki ta Asiya dake gudana a birnin Hangzhou na kasar Sin. Wannan ita ce ziyara ta biyu da shugaba Bashar ya kawo Sin, tun bayan kusan shekaru 20.
A yayin wata zantawa da ya yi cikin shirin tattaunawa da shugabanni, na babban rukunin gidan rediyo da talabijin na kasar Sin(CMG), ya ce, kasar Sin ta samu ci gaba cikin sauri. A da ana kiran kasar Sin da “masana’antar duniya” ko kuma “masana’antar kayayyaki ta duniya,” amma yanzu muna iya cewa, kasar Sin ita ce “masana’antar kirkire-kirkire ta duniya”.
- Amurka Ita Ce “Daular Karya”Ta Ko Wace Fuska
- Kasar Sin Za Ta Kaddamar Da Binciken Duniyar Wata Mai Zuwa A Tsakanin Shekarar 2024
Shugaba Bashar ya jaddada cewa, ko da yake ci gaba da sauye-sauye na da matukar muhimmanci, amma yadda kasar Sin ta ke martaba ka’idoji daya shi ne ya fi muhimmanci. “Ko da ya ke ci gaba da sauye-sauye na iya haifar da wasu illoli, al’adun kasar Sin ba su sauya ba, kuma an san jama’ar kasar Sin da himma ga kasa, da al’umma, kuma al’adu ba su canza ba, wannan ita ce babbar nasara.”
A wannan bazarar, yankin Gabas ta Tsakiya ya samu “guguwar sulhu”. Baya ga komawar Syria cikin kungiyar kasashen Larabawa, bisa shiga tsakani na kasar Sin, kasashen Saudiyya da Iran sun sanar da dawo da huldar jakadanci a tsakaninsu. Dangane da wannan batu, shugaba Bashar ya bayyana cewa, an shafe sama da shekaru 40 ana rikici tsakanin kasashen Saudiyya da Iran a yankin, hakan ya faru ne sakamakon tsarin diflomasiyya na kasashen yamma, musamman salon diflomasiyyar kasar Amurka.
Kasar Amurka na haifar da matsaloli a tsakanin kasashe da dama, sannan ta kwace musu albarkatu domin amfanin kanta. Sanarwar da kasar Sin ta yi na yin sulhu tsakanin kasashen Saudiyya da Iran na nufin cewa, kasar Sin tana daukar matakai na zahiri, ba maganar fatar baki ko farfaganda kamar kasashen yammacin duniya ba, a maimakon haka, tana daukar matakai na siyasa na hakika da kuma samun sakamako.
Shugaba Bashar ya kuma cewa, muna fatan kasar Sin za ta ci gaba da taka rawa a siyasance, kuma kamar yadda muka gani, za ta kara taka muhimmiyar rawa, wadda ke da alaka da kudurorin da shugaba Xi Jinping ya gabatar, ciki har da shawarar samar da tsaro a duniya. Mun yi imanin cewa, wadannan tsare-tsare su ne ka’idodin sabuwar duniya.(Mai fassara: Ibrahim)