Shugaban kasar Syria Bashar al-Assad, ya jinjinawa goyon bayan da kasar Sin ke baiwa kasar sa, da ma irin rawar gani da take takawa, a muhimman batutuwa da suka shafi warware kalubalen da ake fuskanta a gabas ta tsakiya, ciki har da batun warware takaddamar Iran da Saudiyya.
Shugaba Assad ya yi wannan tsokaci ne yayin zantawar sa da jakadan musamman na Sin game da batutuwan gabas ta tsakiya Zhai Jun, ranar Asabar a birnin Damashqa fadar mulkin kasar ta Syria.
Ya ce, “Syria na godewa cikakken goyon bayan Sin, game da batutuwan da suka shafi tabbatar da ‘yancin kan Syria, da ikon kasar na mulkin kai, da kare cikakkun yankunan ta.
A daya bangaren kuma, shugaba Assad ya taya kasar Sin murnar cimma nasarar shiga tsakani, ta yadda aka kai ga warware sabanin dake tsakanin Iran da Saudiyya, yana mai fatan Sin din za ta kara azama, wajen wanzar da daidaito da zaman lafiyar shiyyar. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp