Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya bayyana cewa shugabanci na kwarai ne kadai zai magance matsalolin tsaro da suke addabar shiyyar Arewa maso Yamma, wadanda talauci da fatara hadi da rashin ayyukan yi a tsakanin jama’a suka haddasa.
Gwamnan ya ce, hanya daya tilau na shawo kan wadannan matsalolin shi ne gudanar da shugabanci da mulki na kwarai.
- Babu Inda Na Ce Na Fi ‘Yan Nijeriya Shan Wahalar Tsadar Rayuwa -Ɗangote
- Tsigaggen Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kaduna Liman Ya Sake Lashe Zaben Cike-gurbi
Sani ya shaida hakan ne a gidan gwamnatin Kaduna a lokacin da ya amshi bakwancin kungiyar dattawan Jihar Kaduna a wani ziyarar taya shi murna kan nasarar da ya samu a kotun koli.
A cewar gwamnan, baya ga kokarin da jami’an sojoji ke yi na share dukkanin aikace-aikacen ‘yan fashin daji, ita ma gwamnati ta dukufa wajen gudanar da shugabanci na kwarai a matsayin wani mataki na shawo kan matsalolin tsaro da suke addabar jihar.
Ya kuma ce, “Abubuwan da suka janyo rashin tsaro sun hada da rashin abun yi, rashin ilimi, matsatsin tattalin arziki. Sama da kaso 85 na mutanen arewa maso yamma sun kasance marasa ilimi ko masu fama da talauci.”
“Duk yadda muka yi maganar samar da zaman lafiya, muddin ba mu gudanar da shugabanci na kwarai ba, ba za mu taba shawo kan matsalar tsaro a Nijeriya ba, musamman a arewacin kasar nan.
“Matsalar arewa maso gabas batu ne na mutanen da suka fito daga inda ba a sani ba da maganar akidar Boko.
“Mu kuma a nan talauci ne, idan ba mu shawo kan matsalar ba ta hanyar taimaka wa manomanmu da kara yawan abun da ake nomawa, ba za mu shawo kan matsalar tsaro ba,” gwamnan ya tabbatar.