Kwanan baya, shugabanni da manyan jami’ai daga kasashen duniya da dama sun sauka a birnin Beijing, domin halartar taron kolin mata na duniya, inda suka jinjinawa kasar Sin game da gudummawar da ta bayar domin tabbatar da daidaiton jinsi.
Game da hakan, shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama, ya jinjinawa shugaban kasar Sin Xi Jinping, game da muhimminyar gudummawar da ya bayar domin tabbatar da ci gaban mata. Ya ce, shugaba Xi ya jagoranci gudanar da taron kolin mata na duniya na wannan karo, inda a lokacin aka waiwayi sakamakon da aka cimma a fannin neman ci gaban mata a duniya.
Shugaban na Ghana ya kara da cewa, a matsayin wuri da aka fitar da “Sanarwar Beijing”, kasar Sin ta cimma sakamako mai amfani a fannin baiwa mata iko, musamman ma kan wasu sabbin fannoni da suka hada da aikin sadarwa, da raya sabbin makamashi da dai sauransu.
Haka kuma, shugabar kasar Iceland Halla Tomasdottir ta ce, a matsayin wata babbar kasa, kiran da kasar Sin ta yi yana da muhimmanci ga sauran kasashen duniya. Ayyukan da kasar Sin ta yi a fannin tabbatar da ci gaban mata da daidaiton jinsi, sun kasance abin koyi ga kasashen duniya.
Bugu da kari, shugabar kasar Dominica Sylvanie Burton, ta ce jawabin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi a yayin taron kolin mata na duniya, ya samar da sabon karfi ga raya ci gaban mata bisa dukkan fannoni, kuma kasarta na fatan ci gaba da yin hadin gwiwa da kasar Sin a fannoni da dama. (Mai Fassara: Maryam Yang)