A baya-bayan nan ne shugabannin kasashen Afirka suka aike da sako ga shugaban kasar Sin Xi Jinping, wanda kuma shi ne babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, don taya shi murnar bikin cika shekaru 75 da kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin. Inda shugaban Jamhuriyar Congo Denis Sassou Nguesso ya ce, kasarsa za ta yi duk mai yiwuwa, kuma za ta ci gaba da tsayawa tsayin daka wajen zurfafa hadin gwiwa da kasar Sin, da sa kaimi ga bunkasuwar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.
Kazalika, shugaban kasar Kenya William Ruto ya bayyana cewa, kasar Sin muhimmiyar abokiyar ci gaba ce ga kasashen Afirka, kuma kasar Kenya tana son zurfafa hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare tsakaninta da kasar Sin, domin samun moriyar jama’ar kasashen biyu, da samun wadata tare.
Shi kuma shugaban kasar Zambia Hakainde Hichilema a cewa ya yi, jama’ar kasar Sin sun samu manyan nasarori ta hanyar hadin kai da aiki tukuru, kuma bangaren Zambia na son ci gaba da zurfafa hadin gwiwa da kasar Sin a fannoni daban daban, da gina al’umma mai jituwa da wadata mai makomar bai daya. (Mai fassara: Yahaya)