Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya tattauna ta wayar tarho da takwaransa na kasar Amurka Donald Trump, jiya Alhamis, bisa bukatar da Trump ya gabatar.
Xi Jinping ya ce, ya kamata kasashen biyu su zama jagorori, tare da kawar da matsalolin dake gabansu, domin daidaita dangantakarsu. Bisa rokon da Amurka ta gabatar, masu jagorantar tattaunawar harkokin tattalin arziki da cinikayya na kasashen biyu sun tattauna a birnin Geneva, inda suka taka rawa wajen warware sabanin dake tsakanin Sin da Amurka a fannin tattalin arziki da cinikayya ta hanyar yin shawarwari, lamarin da ya samu amincewa daga bangarori daban daban na kasashen biyu, da ma gamayyar kasa da kasa. Hakan kuma ya nuna cewa, yin shawarwari da hadin gwiwa, ita ce hanya kadai da ya kamata su bi.
Shugaba Xi ya kara da cewa, ya kamata Sin da Amurka su yi amfani da tsarin yin shawarwari kan harkokin tattalin arziki da ciniki da suka kafa da kansu yadda ya kamata, tare da tabbatar da adalci, da girmama matsayar juna, domin cimma moriyar juna. Ya ce kasar Sin tana son bin wannan tsarin, a sa’i daya kuma, tana da ka’idojinta na kanta. A cewar shugaba Xi, idan Sinawa suka yi alkawari, tabbas za su cika.
A halin yanzu, Sin da Amurka sun cimma ra’ayi daya, don haka ya zama dole bangarorin biyu su bi wannan ra’ayi daya da suka cimma.
Bayan tattaunawar da aka yi a birnin Geneva, kasar Sin ta yi aiki bisa yarjejeniyar, don haka ya kamata kasar Amurka ta duba sakamakon da aka samu da idon basira, kuma ta soke matakan da ba su dace ba. Haka kuma, zai fi kyau Sin da Amurka su karfafa mu’amalar dake tsakaninsu kan harkokin diflomasiyya, da tattalin arziki da ciniki, da aikin soja da dai sauransu, domin kara fahimtar juna, da warware sabanin dake tsakaninsu, tare da kuma zurfafa hadin gwiwarsu.
Bugu da kari, Xi Jinping ya jaddada cewa, ya kamata kasar Amurka ta daidaita matsayinta kan batun Taiwan da idon basira, kada masu neman raba yankin Taiwan daga kasar Sin su tura Amurka da Sin cikin rikici.
A nasa bangare, shugaba Trump na Amurka ya ce, yana matukar girmama shugaba Xi Jinping, kuma huldar dake tsakanin Amurka da Sin tana da muhimmanci. Ya ce kasar Amurka ta yi farin cikin ganin karuwar tattalin arzikin kasar Sin. Kana, hadin gwiwar dake tsakanin Amurka da Sin za ta ba da gudummawa ga kasa da kasa. Ya ce a nan gaba kuma, kasarsa za ta ci gaba da bin manufar kasar Sin kasa daya tak a duniya. Bugu da kari, ya ce kasashen biyu sun samu nasarar tattaunawar tattalin arizki da cinikayya a birnin Geneva, inda suka kuma cimma kyakkyawar yarjejeniyar. Kasar Amurka tana fatan hadin gwiwa da kasar Sin wajen aiwatar da yarjejeniyar, haka kuma tana maraba da zuwan daliban kasar Sin.
Kaza lika, shugaba Xi ya yi maraba da Donald Trump ya sake kawowa kasar Sin ziyara, inda shi kuma shugaba Trump ya bayyana godiyarsa matuka. Daga bisani, shugabannin biyu sun cimma matsaya daya kan ci gaba da aiwatar da ra’ayi daya da aka cimma a birnin Geneva, yayin gudanar da sabon zagayen taron tattaunawa. (Mai Fassara: Maryam Yang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp