An kaddamar da bikin baje kolin kayayyakin tarihi na zamanin daular Tang na kasar Sin (karni na 7 zuwa na 10 bayan haihuwar Annabi Isa), a gidan adana kayayyakin tarihi na Musee Guimet dake kasar Faransa, a jiya Litinin, bisa agogon wurin. Kuma shugaban kasar Sin, Xi Jinping, da takwaransa na kasar Faransa, Emmanuel Macron, sun rubuta wasu bayanai, domin a nuna su a wajen bikin.
Cikin bayanin da ya rubuta, shugaba Xi na kasar Sin ya ce, zamanin daular Tang wani lokaci ne da kasar Sin ta samu ci gaba sosai, a dukkan fannonin tattalin arziki, da al’adu, da tunani, da dunkulewar al’ummu. Saboda haka ya yi imanin cewa, jama’ar kasar Faransa, da ta sauran kasashen dake nahiyar Turai, za su fahimci yanayi mai armashi da ake ciki a lokacin daular Tang, da gane ma idanunsu abubuwa masu ban sha’awa dake da alaka da al’adun gargajiya na kasar Sin, ta hanyar halartar bikin baje kolin.
A nasa bangare, shugaba Macron na kasar Faransa ya rubuta cewa, gidan adana kayayyakin tarihi na Musee Guimet ya shirya bikin ne don taya murnar cika shekaru 60 da kulla huldar diplomasiyya tsakanin kasashen Faransa da Sin. A cewarsa, wannan bikin baje koli mai ma’anar tarihi ya nuna yanayi mai kyau da cudanyar kasashen 2 a fannin al’adu take ciki, wadda za ta kara taka mihimmiyar rawa a kokarin kyautata huldar dake tsakanin kasashen 2. (Bello Wang)