Shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na kasar Korea ta Arewa Kim Jong Un, sun yi musayar sakon taya murnar cikar dangantakar diplomasiyya tsakanin kasashensu shekaru 75 da kulluwa.
A cikin sakonsa, shugaba Xi wanda kuma shi ne sakatare janar na kwamitin kolin JKS, ya ce dadaddiyar abota dake tsakanin Sin da Korea ta Arewa ta jure kalubalen duniya da jarabawa, inda ta zama kadara mai daraja ga kasashen biyu da al’ummominsu.
- Ana Shirin Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 18 Ta Jiragen Kasa A Kasar Sin A Yau Lahadi
- Gwamnatin Katsina Ta Sha Alwashin Kare Iyakokin Burtali A Jihar
Ya ce a cikin sabon zamani, a shirye Sin take ta hada hannu da Korea ta Arewa wajen daukar cikar dangatakarsu shekaru 75 a matsayin dama ta karfafa tuntubar juna da hadin gwiwa da zurfafa musaya da hadin gwiwar abota da ci gaba da rubata sabbin babukan tarihin abotarsu, ta yadda za su hada hannu wajen inganta rayawa da inganta ra’ayin gurguzu na kasashen tare da kara amfanawa jama’arsu.
A nasa bangare, shugaba Kim na Korea ta Arewa, ya ce jam’iyyar kasar da gwamnati za su ci gaba da kokarin karfafawa da raya dangantakar abota da ta hadin gwiwa tsakaninsu da Sin kamar dai yadda ake bukata a sabon zamani. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)