A yau juma’a ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da takwaransa na kasar Zambia Hakainde Hichilema a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, inda suka sanar da daga matsayin dangantakar dake tsakanin Sin da Zambia zuwa dangantakar hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare.
Shugaba Hichilema yana ziyarar aiki a kasar Sin ne tun daga ranar 10 zuwa gobe Asabar 16 ga watan Satumba bisa gayyatar da Xi ya yi masa.
Bugu da kari, a yau ne, firaministan kasar Sin Li Qiang shi ma ya gana da shugaban kasar Zambia Hakainde Hichilema dake ziyara a kasar Sin.
A yayin ganawar, Li Qiang ya bayyana cewa, Sin tana son hada kai tare da kasar Zambia wajen aiwatar da muhimman ra’ayoyin da shugabannin kasashen biyu suka cimma, da kara yin hadin gwiwa a tsakaninsu a fannin gina ababen more rayuwa da samar da sabbin fasahohin ci gaban hadin gwiwa a fannonin zamanantar da masana’antu da noma, da samun bunkasuwa ba tare da gurbata muhalli ba, da tattalin arziki na yanar gizo da sauran sabbin fannoni, da samar da hanyar zamanintar da kasashe masu tasowa dake goyon baya ga juna da taimakawa juna da kuma samun farfadowa tare, kana za a tabbatar da moriyar kasashen biyu da ta kasashe masu tasowa baki daya.
A nasa bangare, shugaba Hichilema ya bayyana cewa, an raya dangantakar dake tsakanin Zambia da Sin yadda ya kamata. Kasar Zambia ta kiyaye ka’idar Sin daya tak a duniya, kana tana adawa da wai ra’ayin tarkon bashi, kasar Zambia tana son zurfafa hadin gwiwar dake tsakaninta da kasar Sin a dukkan fannoni don sa kaimi ga samun bunkasuwa tare. (Zainab; Ibrahim Yaya)