Shugabar kungiyar ba da agaji ta kasa da kasa ko ICRC Mirjana Spoljaric Egger ta ce, kasar Sin na taka rawar gani, tana kuma yayata hadin gwiwar sassan kasa da kasa, a fannin tabbatar da nasarar ayyukan jin kai na duniya. Spoljaric ta ce Sin na kara zama muhimmiyar madogara a ayyukan jin kai.
Babbar jami’ar ta ICRC ta bayyana hakan ne a jiya Laraba, yayin wata tattaunawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, a gabar da take gudanar da ziyarar aikinta ta farko a kasar Sin, tun bayan kama aiki a watan Oktoban bara.
Spoljaric ta ce, Sin na cikin kasashen farko farko da suka amince da yarjejeniyar Geneva, da sauran kudurori masu nasaba da ita, ta kuma ci gaba da shiga a dama da ita, wajen sauke nauyin dake wuyan sassan kasa da kasa a fannin ayyukan jin kai.
Jami’ar ta kara da cewa, “A shekarun baya bayan nan, Sin na ci gaba da tura tawagogin likitoci, da jami’an lafiya zuwa kasashe da yankunan dake bukatar agajin jin kai, domin samarwa al’ummun yankunan hidimomin da suke bukata. Wanda hakan ke nuni ga yadda kasar ke mayar da hankali ga tallafawa kasashen waje a fannin kiwon lafiya.”
Daga nan sai Spoljaric ta bayyana Sin a matsayin kasa da ke kan gaba, wajen karbar lambobin karrama jami’an lafiya da suka yi fice, wato “Florence Nightingale Award” karo na 49, wanda hakan ke tabbatar da cewa, ICRC da sauran sassan kasa da kasa, sun gamsu da nasarorin da Sin din ta cimma a fannin ba da tallafin jin kai. (Saminu Alhassan)