Shugabar kwamitin shirya wasannin Olympics na duniya (IOC), Kirsty Coventry, ta halarci bikin bude gasar wasannin kasa ta Sin karo na 15 a lardin Guangdong da yammacin ranar 9 ga Nuwamba. A ranar 12 ga wata kuma, Coventry ta yi wata hira ta musamman da ‘yar jarida daga babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin wato CMG a nan birnin Beijing.
Yayin hirar, Coventry ta bayyana cewa, gasar wasannin kasar Sin ta wannan karo tana da babbar ma’ana. Ta ce yayin da take ziyarar aiki a Sin, ta yi tattaunawa da dama, ciki kuma har da ganawa da shugaba Xi Jinping. Shugaba Xi ya ce mokamar bunkasuwar yankin gabar tekun Guangdong-Hong Kong-Macao, ba tsara manufofin da za a iya cimmawa kadai ya yi ba, har ma da gabatar da alkiblar da za ta tabbatar da cimma hakan a karshe. Ta ce tana fatan wasannin za su iya taka rawa mai tasiri da inganci a cikin wannan tsari.
Ta kara da cewa, a yanzu, wasanni sun zama masana’antar duniya mai daraja sosai. Inda ta ce tana matukar farin cikin ganin jari mai yawa ya shiga cikin harkokin gina al’ummomi. Kuma saka hannun jari a bangaren wasanni, a zahiri saka hannun jari ne a cikin al’umma, kuma yana da muhimmanci ga gina zamantakewa mai kuzari.(Safiyah Ma)













