Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta ce hadin gwiwa tsakanin Sin da Amurka zai amfani sassan 2, yayin da fito-na-fito zai illata su. Ta ce Sin a shirye take ta warware sabani yadda ya kamata da sabuwar gwamnatin Amurka.
Mao ta bayyana hakan ne a Litinin din nan, yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa, lokacin da take amsa tambaya game da abubuwan da Sin ke fatan gani a sabuwar gwamnatin Amurka da za ta fara aiki.
Jami’ar ta kara da cewa, ci gaban dangantakar sassan biyu bisa daidaito, kuma mai dorewa zai amfani moriyarsu, da kuma burikan sauran kasashen duniya. Kaza lika, kasar Sin a shirye take ta yi aiki tare da sabuwar gwamnatin Amurka a fannin ingiza mutunta juna, da bunkasa zaman jituwa, da cimma moriyar juna, da inganta shawarwari da tattaunawa, da fadada hadin gwiwa da zai amfani sassan baki daya, kana da zakulo hanya mafi dacewa ta kyautata tafiyarsu tare.
Game da batun komawa aiki da dandalin TikTok ya yi a Amurka, Mao Ning ta ce ya kamata Amurka ta saurari muryoyin adalci da kyau, ta samar da budaddiyar kofar aiwatar da gaskiya da adalci, da yanayi na gudanar da kasuwanci ba tare da tsangwama ba, ta yadda sassan kasuwannin kasashe daban daban za su iya gudanar da hada-hada yadda ya kamata a kasar. (Saminu Alhassan)