Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya ce Sin na nazarin yanayin da ake ciki game da babban zaben kasar Zimbabwe. Wang wanda ya bayyana hakan a Litinin din nan, yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa, ya ce Sin ta lura da yadda hukumar zaben Zimbabwe ta ayyana shugaban kasar mai ci Emerson Mnangaguva, a matsayin wanda ya lashe zaben da ya gabata.
A daya bangaren, jami’in ya ce Sin a shirye take ta yi aiki da sabuwar gwamnatin Zimbabwe, wajen ingiza ci gaban dangantakar abokantaka ta hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare tsakanin Sin da Zimbabwe.
Wang Wenbin, wanda ya bayyana Zimbabwe a matsayin kawa ta gari ga kasar Sin, ya kuma ce fadada tsarin hadin gwiwar BRICS, zai ingiza ci gaban tsarin jagorancin duniya ta fuskar siyasa da tattalin arziki, ta yadda za a tunkari turba ta gari bisa adalci da hangen nesa.
Bugu da kari, Wang ya kuma bayyana fatan kasar Sin, na ganin Amurka ta martaba kokarin da kasashen yankin suke yi, na wanzar da zaman lafiya da daidaito a sassan tekun kudancin kasar Sin.
Game da shirin kasar Japan bisa radin kan ta, na zubar da ruwan dagwalon nukiliyar Fukushima cikin teku kuwa, Wang Wenbin ya ce kasashe makwaftanta, da ma sauran sassan kasa da kasa na matukar adawa da wannan mataki na son kai, da rashin hangen nesa. (Mai fassara: Saminu Alhassan)