Rahotannin na cewa, an sake samun wani da ya kona Alkur’ani mai tsarki a kasar Sweden, lamarin da al’ummun kasashen Larabawa, da sauran musulmin duniya suka yi matukar Allah wadai da shi, yayin da kuma al’ummun kasa da kasa ke nuna damuwa da aikata hakan.
Da take tsokaci kan hakan, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta ce har kullum kasar ta na yayata akidar martaba juna, da tafi tare da dukkanin sassa, da koyi da juna tsakanin mabanbantan wayewar kai. Kaza lika Sin na adawa da duk wani tsattsauran ra’ayi na kaiwa addinai hari, ko tunzura fito na fito tsakanin al’ummu, ko kyamar musulunci.
Mao, wadda ta bayyana hakan yayin taron manema labarai na Talatar nan, ta ce wayewar kan musulunci ta bayar da gagarumar gudummawa ga ci gaban duniya, kuma ya zama wajibi a martaba akidun musulunci da musulmi. A daya hannun, bai kamata a fake da ‘yancin fadin albarkacin baki wajen rura wutar tashin hankali tsakanin mabanbantan wayewar kai ba.
A watan Maris din shekarar nan ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gabatar da shawarar bunkasa wayewar kai tsakanin al’ummun kasa da kasa, inda ya yi kira da a aiwatar da manufofin daidaito, da koyi da juna, da tattaunawa, da tafiya tare tsakanin dukkanin wayewar kan al’ummun duniya.
Kasar Sin ta shirya tsaf, ta yi aiki da sauran sassan kasa da kasa, wajen yayata ruhin wannan shawara ta bunkasa wayewar kai tsakanin al’ummun duniya, da ingiza musaya tsakanin mabanbantan al’adu, da cimma matsaya ta aiwatar da matakai na hakika, da hada gwiwa wajen kare kimar mabanbantan wayewar kan al’ummun duniya. (Saminu Alhassan)