Mataimakin firaministan kasar Sin Zhang Guoqing, ya ce Sin a shirye take, ta yi karin hadin gwiwa mai ma’ana, da cimma moriya tare da sauran kasashe a fannin kare ikon mallakar fasaha, ta yadda hakan zai amfani karin kasashe da al’ummun su.
Zhang ya bayyana hakan ne jiya Asabar, cikin jawabin da ya gabatar yayin bikin bude dandalin kasa da kasa na kungiyar kare ikon mallakar fasaha na shekarar nan ta 2024. (Mai fassara: Saminu Alhassan)