Yau Talata ne aka fara gudanar da jarrabawar shiga jami’a a sassa daban daban na kasar Sin.
Alkaluman ma’aikatar ilmi ta kasar Sin sun nuna cewa, yawan wadanda suka yi rajistar rubuta jarrabawar a bana ya kafa tarihi, inda ya kai miliyan 11.93 baki daya, wanda ya karu da miliyan 1 da dubu 150 bisa na shekarar 2021.
Akwai wuraren gudanar da jarrabawar guda dubu 330 a duk fadin kasar Sin, tare da masu sa ido kimanin miliyan 1 da dubu 20. (Tasallah Yuan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp