Alkaluman da kamfanin zirga-zirgar jiragen kasa na kasar Sin wato China Railway ya gabatar, sun nuna cewa, ana sa ran jigilar fasinjoji kimanin miliyan 21 da dubu 750, ta jiragen kasa a kasar Sin a yau Laraba. Kana tun daga ranar 29 ga watan Satumban da ya gabata, wato ranar da aka kaddamar da aikin jigilar fasinjojin da suka yi tafiye-tafiye, a lokacin hutun bikin tunawa da kafuwar kasa da na Zhong-Qiu, zuwa jiya Talata, an riga an kwashe fasinjoji fiye da miliyan 160 ta jiragen kasa a kasar Sin.
Yau ce ranar karshe a hutun na wannan karo, don haka ake sa ran ganin karuwar zirga-zirgar mutane da suke kokarin komawa gidajensu daga wuraren da suka yi bulaguro. Hakan ne kuma ya sa ake amfani da karin jiragen kasa wajen samar da hidimar sufuri ga fasinjoji, inda ake sa ran ganin aiki ya gudana da karin jiragen kasa 2,189 a yau, a wurare daban daban na kasar Sin. (Bello Wang)