Yayin da kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta amsa tambayoyi game da makomar hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka, ta bayyana cewa, a halin yanzu, ana fuskantar kalubale a duniya, kuma a matsayin kasa mai tasowa mafi girma da nahiyar da ta fi samun kasashe masu tasowa, Sin da Afirka sun fi bukatar kara hadin gwiwa da juna. Ta ce Sin tana son yin kokari tare da kasashen Afirka, da bin ra’ayin bangarori daban daban, da tabbatar da moriyarsu, da sa kaimi ga zamanintar da su, da yin kwaskwarima kan tsarin sarrafa harkokin duniya, da neman samun tsaro, da yin mu’amalar al’adu da juna, da gina al’ummomin Sin da Afirka mai makoma ta bai daya, da kuma zama misali na raya al’umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil’Adama.