Tawagogin Sin da Amurka sun yi tattaunawar keke-da-keke, mai ma’ana da zurfi bisa girmama juna da daidaito, dangane da batutuwan tattalin arziki da cinikayya dake ci musu tuwo a kwarya, ciki har da batun TikTok.
Yayin wani taron manema labarai, Li Chenggang, wakilin Sin kan harkokin cinikayya da kasa da kasa kuma mataimakin ministan kula da cinikayya na kasar, ya ce bangarorin biyu sun amince cewa, kyakkyawar dangantaka tsakanin kasashensu na da matukar muhimmanci, kuma tana da gagarumin tasiri kan ci gaban tattalin arzikin duniya da gudanarsa ba tare da tangarda ba.
Game da batun TikTok, Li Chenggang ya ce, har kullum, Sin ta kasance mai adawa da siyasantarwa da amfani da fasaha da ma tattalin arziki da cinikayya a matsayin makami, kuma ba za ta taba cimma yarjejeniya bisa watsi da akidu ko muradun kamfanoninta ko kuma adalci da daidaito na duniya ba.
Yayin taron, bangarorin biyu sun yi tattaunawa mai zurfi game da batun na TikTok da sauran batutuwa masu ruwa da tsaki, kuma sun cimma matsayar warware batun na TikTok ta hanyar hadin gwiwa, da rage shingen zuba jari da inganta hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya.
Bugu da kari, bangarorin biyu sun amince da ci gaba da tuntubar juna, da tattaunawa game da sakamakon daftarorin tattaunawar, kuma dukkansu za su fara shirye-shiryen aiwatar da su a cikin gida. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp