A cikin shekaru 10 da suka gabata, hadin gwiwar cimma moriyar juna tsakanin Sin da kasashen Afirka ya bunkasa zuwa matsayin inganci, inda kamfanonin Sin da dama suka aiwatar da mayan ayyukan samar da ababen more rayuwa da dama, da hadin gwiwar samar da makamashi mai tsafta a sassan Afirka, yayin da kuma albarkatun gona daga kasashen Afirka ke kara shiga cimakar kasar Sin. Wannan yanayi ya kara tabbatar da matsayar sassan biyu, ta kafa al’umma mai makomar bai daya.
Wani abun tambaya ma shi ne ko mene ne dalilin da ya sa Sin da kasashen Afirka ke kara dunkulewa waje guda ta fuskar hadin gwiwa? Ko shakka babu dalilin bai tsaya ga batun amincewa juna a tafarkin ‘yantar da kai da sassan biyu suka yiwa juna ba ne, har akwai batun burin da suke da shi na zamanantar da kai, da sauke nauyin kare moriyar bai daya ta kasashe masu tasowa, tare da neman cimma daidaito, da adalci tsakanin sassan kasa da kasa.
Taron FOCAC na 2024 da ke tafe, zai haskaka sabon matsayin alakar Sin da kasashen Afirka, da ingiza sabon kuzari ga yunkurin su na zamanantar da kai. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp