Kasar Sin da Rasha za su yi aiki tare don fadada hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasashen biyu, a cewar sanarwar hadin gwiwa da aka fitar jiya Laraba, bayan ganawar shugabannin kasashen Sin da Rasha karo na 29.
Firaministan kasar Sin Li Qiang da firaministan kasar Rasha Mikhail Mishustin ne suka jagoranci taron tare.
- An Samu Nasarori Da Dama Kan Hadin Gwiwar Tattalin Arziki Da Cinikayya A Tsakanin Sin Da Afirka
- Shugaban Kasar Sin Ya Bukaci A Daukaka Ra’ayin Gurguzu Mai Sigar Kasar Sin Yayin Da Deng Xiaoping Ke Cika Shekaru 120 Da Zuwa Duniya
Sanarwar ta ce, bangarorin biyu sun amince da cewa, za a yi kokarin hadin gwiwa wajen kyautata tsarin cinikayya, da samar da sabbin fasahohin bunkasar tattalin arzikin da yawan cinikayya tsakanin kasashen biyu, da inganta ci gaban cinikayya ta yanar gizo.
Bangarorin biyu sun kuma amince da cewa, za a ba da goyon baya ga kasashen BRICS a hadin gwiwarsu a fannonin inganta kwarewar aiki, da bincike na hadin gwiwa, da gudanar da harkokin duniya a fannin amfani da fasashohi masu kwaikwayon tunanin dan Adam. (Mai Fassara : Mohammed Yahaya)