Kasashen Sin da Rasha sun sha alwashin karfafa hadin gwiwarsu don kare karfin ikon dokokin duniya, kamar yadda wata sanarwar hadin gwiwa da suka fitar a jiya Alhamis ta bayyana.
Sanarwar ta kara da cewa, kasashen biyu sun yi alkawarin tabbatar da bin tsarin kasa da kasa a karkashin ikon Majalisar Dinkin Duniya (MDD) da kuma dokokin duniya da aka amince da su a tsakanin kasa da kasa, da kuma kare muhimmiyar rawar da MDD ke takawa a harkokin kasa da kasa.
- Shugaban Kasar Sin Xi Jinping Ya Halarci Bukukuwan A Moscow
- Waiwaye Game Da Gudummawar Shawarar BRI Ga Duniya
Kazalika, kasashen biyu sun ce dole ne a yi la’akari da gaskiyar yanayin da duniya ke ciki mai kunshe da mabambantan kasashe a bisa jagorancin MDD yayin da ake yin gyare-gyare da inganta dokokin kasa da kasa. Kuma Sin da Rasha sun goyi bayan fadada shigar da dukkan kasashe cikin yarjejeniyoyin MDD, da samar da fahimta iri daya da kuma amfani da su yadda ya kamata.
Bugu da kari, kasashen biyu sun sake nanata cikakken alkawarinsu kan aiki da tsarin dokoki na Majalisar Dinkin Duniya, da matsayar da aka cimma tare da ayyanawa a shekarar 1970 game da bin ka’idojin dokokin kasa da kasa, dangane da kyakkyawar hulda da hadin gwiwar kasashe a karkashin tsarin dokokin MDD da kuma la’akari da yanayin tsari da alakokin muhimman ka’idojin dokokin kasa da kasa da aka bayyana a cikin ayyananniyar matsayar da aka cimma.
Har ila yau, kasashen biyu sun sake jaddada cewa, bai kamata kasashe su rika karya ka’idar tsarin dokokin MDD da ta haramta yin barazana ko amfani da karfin soji ba, don haka suka yi Allah wadai da daukar matakin soji da bangare daya ke yi wanda ya yi hannun riga da hujjar kare kai ta daidaikun kasashe ko ta kasashe masu yawa ko kuma ba ta hanyar da kudurorin da kwamitin sulhun MDD ya amince da su a karkashin babi na 7 na tsarin ba. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp