• English
  • Business News
Thursday, October 30, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sin Da Uganda Na Sa Ran Karfafa Hadin Gwiwarsu A Fannin Gina Ababen More Rayuwa Ga Kirkire-Kirkire

by CMG Hausa
3 years ago
Sin

Jiya Alhamis ne aka gudanar da taron murnar cika shekaru 60, da kafuwar huldar diflomasiyya tsakanin kasar Sin da kasar Uganda ta kafar bidiyo.

A yayin taron, mataimakin shugaban kungiyar sada zumunci da kasashen waje ta kasar Sin Jiang Jiang, ya bayyana cewa, a halin yanzu, ya kamata kasar Sin da kasashen Afirka su hada kansu, wajen karfafa hadin gwiwa a fannonin gina ababen more rayuwa, da gudanar da kirkire-kirkire ta fuskar harkokin sadarwa, da neman bunkasuwa ta hanyar kare muhalli, domin neman babban ci gaba.

  • ’Yan Sama Jannati Na Kasar Sin Sun Gayyaci Matasan Duniya Da Su Ziyarci Tashar Sararin Samaniyar Sin

A nata bangare, jakadar kasar Uganda dake kasar Sin Oliver Wonekha ta bayyana cewa, shekarar 2022 wata muhimmiyar shekara ce, domin a cikin ta ake cika shekaru 60 da kafuwar huldar diflomasiyya a tsakanin kasar Uganda da kasar Sin, kuma cikin wadannan shekaru da suka gabata, ana ci gaba da zurfafa dangantakar abokantaka a tsakanin kasashen biyu, yayin da aka cimma sakamako da dama.

Tana mai cewa, “Kasar Sin ta kasance daya daga cikin kasashen da suka fi zuba jari a kasar Uganda, wanda hakan ta taka muhimmiyar rawa a fannin raya tattalin arzikin kasar Uganda, shi ya sa, gwamnatin kasar take godiya matuka dangane da taimakon da kasar Sin ta samar mata.

Kaza lika kasar Sin ta samar da taimakon kudi ga wasu muhimman shirye-shiryen raya kasar Uganda, kamar na gina tashar samar da wutar lantarki da karfin ruwa ta Karuma, da gina manyan hanyoyin mota tsakanin birnin Entebbe da birnin Kampala da sauransu.

LABARAI MASU NASABA

Sakamakon Nazarin CGTN Ya Yabawa Gudunmuwar Sin Ga Dunkulewar Yankin Asiya Da Pasifik

Sabon Ingantaccen Hadin Gwiwar “Sin-ASEAN 3.0″ Ya Kafa Sabon Misali Na Hadin Kan Yanki

Kuma, bisa bayanin da aka fidda, ya zuwa shekarar 2020, karfin cinikayya a tsakanin kasashen biyu, ya zarce dallar Amurka har biliyan 1.

Kasar Sin ta kuma ba da gudummawa matuka ga kasar Uganda, a fannin gudanar da kwaskwarima, da neman ci gaba, bisa tsarin dandalin tattauna hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka wato FOCAC”. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Sakamakon Nazarin CGTN Ya Yabawa Gudunmuwar Sin Ga Dunkulewar Yankin Asiya Da Pasifik
Daga Birnin Sin

Sakamakon Nazarin CGTN Ya Yabawa Gudunmuwar Sin Ga Dunkulewar Yankin Asiya Da Pasifik

October 29, 2025
Sabon Ingantaccen Hadin Gwiwar “Sin-ASEAN 3.0″ Ya Kafa Sabon Misali Na Hadin Kan Yanki
Daga Birnin Sin

Sabon Ingantaccen Hadin Gwiwar “Sin-ASEAN 3.0″ Ya Kafa Sabon Misali Na Hadin Kan Yanki

October 29, 2025
An Yi Taron Tataunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Moscow, Manama, Da Budapest
Daga Birnin Sin

An Yi Taron Tataunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Moscow, Manama, Da Budapest

October 29, 2025
Next Post
‘Yan Bindiga Sun Farmaki Hadimin Gwamnan Bauchi, Sun Jikkata Mutum 1

'Yan Bindiga Sun Farmaki Hadimin Gwamnan Bauchi, Sun Jikkata Mutum 1

LABARAI MASU NASABA

Sin

Bai Kamata Gwamnati Ta Ke Ciyo Bashi Bayan Cire Tallafin Man Fetur Ba – Sanusi II

October 30, 2025
Tinubu Ya Gaza Wajen Magance Matsalar Tsaro A Nijeriya — Atiku

Atiku Ya Soki Gwamnatin Tinubu Kan Sauya Sunayen Waɗanda Aka Yi Wa Afuwa

October 30, 2025
Sakamakon Nazarin CGTN Ya Yabawa Gudunmuwar Sin Ga Dunkulewar Yankin Asiya Da Pasifik

Sakamakon Nazarin CGTN Ya Yabawa Gudunmuwar Sin Ga Dunkulewar Yankin Asiya Da Pasifik

October 29, 2025
Asuu

Gwamnatin Tarayya Ta Saki Naira Biliyan 2.3 Ga ASUU

October 29, 2025
Sabon Ingantaccen Hadin Gwiwar “Sin-ASEAN 3.0″ Ya Kafa Sabon Misali Na Hadin Kan Yanki

Sabon Ingantaccen Hadin Gwiwar “Sin-ASEAN 3.0″ Ya Kafa Sabon Misali Na Hadin Kan Yanki

October 29, 2025
Sulhu Da ’Yan Bindiga Ba Tare Da Sun Ajiye Makamai Ba Tamkar Miƙa Wuya Ne – Gwamna Lawal ga Hukumomin Tsaro

Sulhu Da ’Yan Bindiga Ba Tare Da Sun Ajiye Makamai Ba Tamkar Miƙa Wuya Ne – Gwamna Lawal ga Hukumomin Tsaro

October 29, 2025
An Yi Taron Tataunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Moscow, Manama, Da Budapest

An Yi Taron Tataunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Moscow, Manama, Da Budapest

October 29, 2025
majalisar kasa

Majalisar Wakilai Ta Amince Da Bukatar Amso Bashin Dala Biliyan 2.34 A Kasuwar Jari Ta Duniya

October 29, 2025
An Samu Ingantuwar Yanayin Iska Da Ruwa Cikin Watanni 9 Na Farkon Bana A Sin

An Samu Ingantuwar Yanayin Iska Da Ruwa Cikin Watanni 9 Na Farkon Bana A Sin

October 29, 2025
Kotu Ta Umarci Ƙwace Dala 49,700 Daga Tsohon Jami’in INEC

Kotu Ta Umarci Ƙwace Dala 49,700 Daga Tsohon Jami’in INEC

October 29, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.