A jiya Litinin ne kasashen Sin da Zambiya suka rattaba hannu kan wata yarjejeniya kan fitar da kwarurun macadamia nuts zuwa kasar Sin.
Bikin rattaba hannu kan yarjejeniyar ya samu halarcin mukaddashin jakada na ofishin jakadancin Sin da ke Zambiya Wang Sheng, da ministan noma na kasar Zambiya Mtolo Phiri.
- Kano Pillars Ta Janye Dakatarwar Da Ta Yi Wa Kocinta, Usman Abdallah
- Farashin Man Fetur Ya Ƙara Tashi Sakamakon Rikicin Dangote Da NNPCL
A jawabinsa, Wang ya bayyana cewa, rattaba hannu kan yarjejeniyar ya kasance wani babban mataki na bude kasuwar kasar Sin ga kwayoyi dangin gyada na kasar Zambiya, wanda zai amfanar da manoman kasar nan gaba ba da jimawa ba. Ya kara da cewa, baya ga wannan yarjejeniyar da wata ta daban da aka cimma a baya kan fitar da ‘ya’yan itace na blueberry daga Zambiya zuwa kasar Sin, ana kuma ci gaba da shawarwarin fitar da sauran kayayyakin amfanin gona, kamar busasshen paprika da avocado zuwa kasar ta Sin.
Yarjejeniyar dai wani muhimmin sakamako ne na taron dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afirka da aka gudanar a birnin Beijing a watan Satumban bara, lokacin da kasar Sin ta bayyana kudurinta na soke haraji kashi 100 bisa 100 kan kayayyakin dukkan kasashe masu karancin ci gaba, wadanda take da huldar diflomasiyya da su, ciki har da kasar Zambiya. (Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp