Kwanan baya, jagoran yankin Taiwan na kasar Sin Lai Ching-te ya gabatar da jawabai masu taken wai “jawabai 10 game da hadin kan al’umma”, da nufin ba da ingantacciyar hujja ga ra’ayinsa na shirme game da ballewar Taiwan daga kasar Sin, tare da yaudarar jama’ar yankin da kuma sauran al’ummun duniya.
Kowa ya san yankin Taiwan wani bangare ne da ba za a iya raba shi da kasar Sin ba, kuma wannan shi ne matsaya daya da al’ummun Sinawa da yawansu ya kai biliyan 1.4 ciki har da jama’ar yankin Taiwan da yawansu ya kai miliyan 23 suka dauka, wanda kuma ra’ayi ne daya tilo da kasashen duniya suka cimma matsaya a kai.
Sanawar Alkahira da sanarwar Potsdam da dai sauran takardun shari’a sun aza ingantaccen tubali ga dokar kasa da kasa dake bayyana cewa, Taiwan yankin jamhuriyyar jama’ar kasar Sin ne da ba za a iya ware shi ba. Ban da wannan kuma, MDD ta zartas da kuduri mai lamba 2758 a shekarar 1971, inda matakin ya sake nanata kasancewar Taiwan a matsayin wani yanki na kasar Sin. Kuma, karkashin jagorancin wannan kuduri, yawancin kasashe sun katse hulda da mahukuntan yankin Taiwan, inda suka amince da halastaccen matsayin gwamnatin jamhuriyar jama’ar kasar Sin kawai a duniya. Hakan ya sa, ra’ayin kasancewar kasar Sin daya tak a duniya ya samu amincewa daga al’ummun duniya, kuma ya zama ka’idar tushe ta huldar kasa da kasa.
Yunkurin da wasu mutane kamar su Lai ke yi kamar tururuwa ce a gaban giwa, watau karamar alhaki ce da ba ta isa komai ba. (MINA)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp