Wasu rahotanni sun nuna cewa, shugaban kasar Koriya ta kudu Yoon Seok-Youl, ya gabatar da wani jawabi a majalisar dokokin kasar Amurka a kwanan baya, inda ya bayyana cewa, Amurka tana kokarin dakile kalubale, domin tabbatar da ‘yancin kanta a cikin shekaru 100 da suka gabata, kuma sojojin kasar sun samu sakamako mai ban mamaki a yakin tafkin Changjin a shekarar 1950, duk da cewa, sojojin kasar Sin sun fi su yawa sosai.
Kan wannan batu, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta mayar da martani a jiya Jumma’a, tana mai cewa, ta lura da kalaman shugaban Koriya ta kudu, kuma ta jaddada cewa, babbar nasarar da sojojin kasar Sin suka samu yayin yakin adawa da Amurka, wanda suka gwabza domin taimakawa Koriya ta arewa, yana da babbar ma’ana mai zurfi ga ita kanta, gami da duk duniya baki daya, saboda nasarar hakan ta shaida wa daukacin al’ummomin kasa da kasa cewa, duk wanda yake fatan hana ci gaban tarihi, ba zai yi nasara ba.
Takardun tarihin yakin tafkin Changjin sun nuna cewa, gaba daya, adadin abokan gaba da sojojin kasar Sin suka kashe yayin yakin ya kai dubu 36, ciki har da sojojin kasar Amurka dubu 24. (Mai fassarawa: Jamila)