Yayin da hada-hadar tattalin arziki ke kara komawa zuwa yanayi makamancin gabanin bullar anobar COVID-19 a nan kasar Sin, harkokin tafiye-tafiye, da yawon bude ido, da sayayya na kara farfadowa, a rubu’in farko na shekarar nan ta 2023.
Alkaluma sun nuna cewa, hada-hada ta kara bunkasa a filin jirgin saman kasa da kasa na Baiyun na Guangzhou, wanda ya zamo kan gaba a dukkanin kasar Sin a fannin zirga-zirgar jiragen sama cikin watanni ukun farkon shekarar ta bana. Alkaluman sun nuna cewa, cikin wannan wa’adi, fasinjoji miliyan 13 sun yi zirga-zirga ta jiragen sama 105,000. Adadin fasinjojin da ya kai karuwar kaso 61 bisa dari, kan na rubu’in farko na shekarar 2022, kana adadin jiragen da suka yi jigilar fasinjoji tsakanin wa’adin ya karu da kaso 22 bisa dari a tsakanin wannan lokaci.
Sakamakon wannan ci gaba, filayen jiragen sama daban daban, sun fara bude shaguna, da dakunan cin abinci, wadanda yawan su ya kai na gabanin bullar annobar COVID-19. A filin jiragen saman kasa da daka na Hongqiao na Shanghai, an bude sama da shaguna 140, adadin da kai kusan wadanda ake da shi a shekarar 2019.
Kaza lika, wasu alkaluma da bankin al’umma na kasar Sin ya fitar a ranar Litinin, sun nuna yadda adadin sayayya da Sinawa ke yi a yanzu ta karu da babban matsayi, wanda ya dace da na lokacin farfadowa daga annobar.
Alkaluman da bankin ya fitar sun nuna aniyar kaso daya bisa hudu, na kwastomomin bankunan kasar 20,000 dake biranen kasar 50, ta kara yawan kudaden da suke kashewa a rubu’in farko na shekarar ta bana, adadin da ya dan karu kan na rubu’in karshen shekarar bara. (Saminu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp