An cimma wani kunshin yarjejeniyoyin sauyin yanayi da sanyin safiyar Lahadi a gun taron kasashem da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar sauyin yanayi ta MDD karo na 29 wato COP 29.
Yarjejeniyoyin sun hada da shawarwari kan sabuwar manufar ba da kudade daga rukunoni kan harkokin da suka shafi yanayi wato NCQG, da batutuwan da suka shafi tsarin kasuwancin carbon na duniya a karkashin sashe na 6 na yarjejeniyar Paris.
- Farashin Kayayyaki Ya Yi Tashin Gwauron Zabi A Birtaniya Saboda Tsadar Makamashi
- Tinubu Ya Dawo Abuja Bayan Halartar Taron G20 A Kasar Brazil
A cikin jawabinsa yayin rufe taron, shugaban tawagar kasar Sin, kuma mataimakin ministan muhalli da muhallin halittu na kasar Sin Zhao Yingmin, ya jaddada cewa, bil Adama al’umma ce mai makomar bai daya, kuma a yayin da ake fuskantar matsalar sauyin yanayi, hadin kai da hadin gwiwa kadai su ne hanyoyi masu dacewa.
Har ila yau Zhao ya bayyana cewa, cimma manufar NCQG ta bayyana cewa, alkawurran da kasashen da suka ci gaba suka dauka wajen samar da kudade har yanzu ba su kai ga cimma bukatun kasashe masu tasowa ba, kuma dole ne a kara fayyace nauyin da ya rataya a wuyansu na samar da kudade.
Zhao ya kara cewa, kasar Sin, a matsayinta na babbar kasa mai tasowa kuma mai sanin ya kamata, za ta ci gaba da sa kaimi ga tabbatar da tsarin bangarori daban daban da yin hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa kan sauyin yanayi, ba tare da la’akari da yadda yanayin duniya ke tafiya ba. Zhao ya kuma bayyana cewa, kasar Sin za ta ci gaba da aiwatar da manyan tsare-tsarenta na kasa da kasa don tinkarar matsalar sauyin yanayi, da aiwatar da manufofinta na kaiwa kololuwar fitar da iskar carbon dioxide da daidaita hayakin da ake fitarwa da wanda ke cikin sararin samaniya, da sa kaimi ga yin hadin gwiwa da kasashe masu tasowa kan sauyin yanayi, don ba da gudummawa ga kiyaye muhallin duniya, da karancin hayakin carbon, da jurewar yanayin duniya mai dorewa. (Mohammed Yahaya)