Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana cewa, raya hadin kai da hadin gwiwa da kasashen Afirka muhimmin tushe ne na manufofin harkokin wajen kasar Sin, kuma shi ne zabin Sin na dogon lokaci bisa manyan tsare-tsare.
A yayin taron shugabannin kasashen BRICS da za a gudanar a mako mai zuwa, shugaban kasar Sin Xi Jinping zai jagoranci taron shugabannin kasashen Afirka da Sin da takwaransa na Afirka ta Kudu Matamela Cyril Ramaphosa, tare da gayyatar shugabannin kasashen Afirka na dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka, da shugabannin karba-karba na kungiyar tarayyar Afirka. da wakilan kungiyoyin shiyar Afirka da za su halarci taron.
Kasashen Sin da Afirka za su samar da makoma mai kyau ga al’ummominsu, ta hanyar gado da kuma ciyar da dangantakar abokantaka tsakanin Sin da Afirka gaba, da samar da kyakkyawan sakamako na hadin gwiwa, da zama abin koyi wajen raya al’umma mai kyakkyawar makoma ga daukacin bil-Adama.
Wang Wenbin ya bayyana cewa, a yayin ziyarar, shugaba Xi zai yi musayar ra’ayi da shugaba Ramaphosa kan dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, da batutuwan kasa da kasa da na shiyya-shiyya, za kuma su tattauna kan tsarin raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, da kara azama mai karfi wajen gina wata babbar al’umma mai kyakkyawar makoma tsakanin Sin da Afirka ta Kudu.(Ibrahim)