Ma’aikatar kula da cinikayya ta kasar Sin ta bayyana a yau cewa, katsalandan din da gwamnatin Netherlands ta yi cikin harkokin cikin gida na kamfanin Nexperia, ya haifar da tsaiko ga tsarin ayyukan masana’antu da na samar da kayayyaki na duniya.
Kakakin ma’aikatar ne ya bayyana haka lokacin da aka nemi jin ta-bakinsa kan batu na baya bayan nan da ya shafi kamfanin Nexperia mai samar da na’urorin semiconductor, wanda wani reshe ne na kamfanin kasar Sin na Wingtech, dake aiki a kasashen ketare.
A cewar kakakin, a matsayin kasar da ta san ya kamata, Sin na la’akari da batun tsaro da amincin tsarin ayyukan masana’atu da na samar da kayayyaki na cikin gida da kuma na duniya.
Ya ce Sin tana maraba da kamfanonin dake fuskantar kalubale su tuntubi ma’aikatar ko hukumomi masu ruwa da tsaki, yana cewa, ma’aikatar za ta nazarci ainihin abubuwan dake faruwa da kuma bayar da damar fitar da kayayyaki ga wadanda suka cancanta. (Mai fassara: FMM)














