Shugaban majalissar dattijan janhuriyar dimokaradiyyar Congo DRC Modeste Bahati Lukwebo, ya ce kasar Sin kyakkyawan misali ce ga kasar sa. Mista Lukwebo, ya bayyana hakan ne a jiya Juma’a, yayin da yake jawabi ga mahalarta liyafar da aka shirya, a ofishin jakadancin Sin dake kasar, albarkacin cikar janhuriyar al’ummar kasar Sin shekaru 74 da kafuwa.
Ya ce Sin ta cimma manyan nasarori a shekaru 10 da suka gabata, ta kuma zama abun koyi ga janhuriyar dimokaradiyyar Congo. Mista Lukwebo ya kara da cewa, kowa na sanya ido kan sauye sauye masu ban mamaki da Sin ke samu, inda kasar ta cimma manyan nasarori a fannonin raya tattalin arziki, da yaki da fatara, da ci gaban fasahohi ta hanyar aiki tukuru da da’a, don haka Sin ta kasance misali mai kyau da ya dace al’ummar kasar sa su kwaikwaya.
Daga nan sai Lukwebo ya tabo batun ziyarar da shugaban janhuriyar dimokaradiyyar Congo Felix Tshisekedi ya gudanar a kasar Sin a watan Mayun bana, ziyarar da ya ce ta ingiza hadin gwiwar kasashen biyu a fannoni daban daban, wanda hakan ke nuna yadda janhuriyar dimokaradiyyar Congo ke nacewa matsayin ta na hadin gwiwa da Sin. (Mai fassara: Saminu Alhassan)