Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta bayyana a yayin taron manema labarai na yau da kullum Jumma’ar nan cewa, kasar Sin tana mai da hankali matuka kan hasarar rayuka da dukiyoyi da mahaukaciyar guguwar da ta afkawa gabashin Libya ta haifar.
A ranar 11 ga watan Satumba ne, mahaukaciyar guguwar Daniel ta haddasa mummunar ambaliyar ruwa a gabashin kasar Libya, inda ya zuwa yanzu mutane da dama suka mutu, yayin da sama da mutane dubu 10 suka bace, ana kuma sa ran adadin wadanda suka mutu zai karu.
Mao Ning ta kara da cewa, domin agazawa kasar Libya yaki da matsalar ambaliyar ruwa, kungiyar agaji ta Red Cross ta kasar Sin ta sanar da bayar da taimakon kudi na gaggawa ga kungiyar ba da agaji ta Red Crescent ta kasar Libya, kuma kasar Sin tana kara kaimi ga ayyukan jin kai ga bangaren kasar Libya, kuma tana son ci gaba da taimakawa kasar Libya, don taimakawa al’ummar Libya shawo kan matsaloli tare da sake gina gidajensu nan da nan daidai da bukatun bangaren Libya. (Ibrahim)