Ya zuwa yanzu, hukumomin tabbatar da tsaron kasar Sin sun gina cibiyoyin ayyukan wanzar da tsaro har 3,055, wadanda ake amfani da su wajen tsaro, da lura da korafe-korafe a sassan kasar baki daya.
A cewar ma’aikatar tsaron al’umma ta Sin ko MPS a takaice, sama da ‘yan sanda miliyan 1.9 ne ke da shaidar kwarewa a matakin farko, yayin da karin wasu 60,000 ke da shaidar kwarewa a babban mataki.
- Kasar Sin Ta Zama Babbar Kasa A Fannin Kiyaye Ikon Mallakar Fasaha Kuma Muhimmin Jigo A Fagen Kirkire-kirkire A Duniya
- Jarin Sin Ya Bunkasa Sashen Sabbin Makamashi A Zimbabwe
Kaza lika a cewar MPS, hukumomin tsaron Sin na ci gaba da daga matsayin kwarewar su a fannin ginawa, da cimma gajiya daga cibiyoyin jagorancin tsaro, ta yadda cibiyoyin za su samar da hidimomin tsaro daban daban.
Har ila yau, ana kara azama wajen gina tsarin tsaro mai inganci, bisa doka, mai karfi, da nagarta, kana ana aikin fadada inganci, da fa’ida, da ingiza nasarar ayyuka masu nasaba. (Saminu Alhassan)