Wasu alkaluma da ma’aikatar raya masana’antu da fasahar sadarwa ta kasar Sin ta fitar sun nuna cewa, ya zuwa karshen watan Satumban da ya shude, adadin tashoshin fasahar sadarwa na 5G da aka kafa a Sin, sun kai miliyan 3.19, adadin da ya ingiza ci gaban sashen tattalin arziki mai nasaba da fasahar sadarwa a kasar.
Yayin wani taron manema labarai, kakakin ma’aikatar Zhao Zhiguo ya ce, duk Sinawa 10,000 na amfani da tashoshin 5G 22.6. (Mai fassara: Saminu Alhassan)