A baya bayan nan, wurare daban-daban na kasar Sin na fitar da manufofi da matakai daban-daban, don taimakawa kamfanoni wajen tinkarar kalubaloli da inganta kasuwanni, ta yadda za a ingiza farfadowar tattalin arzikin Sin.
Birnin Guangzhou na tallafawa ayyukan samar da kayayyaki da aka zuba jarin da yawansa ya wuce RMB Yuan biliyan 1. Ban da wannan kuma, yankin Xicheng na birnin Beijing, ya fitar da manufar kara karfin taimakawa manyan sana’o’i, da kuma samarwa wasu muhimman hukumomi tallafin kudi da yawansu ya kai RMB Yuan miliyan 50, da samar da kudin rangwamen hayar gidaje har kashi 50% cikin shekaru uku masu zuwa. Kaza lika, lardin Heilongjiang da Jiangxi da sauransu, sun samar da takardun sayayya, don karawa al’umma kwarin gwiwar sayen abubuwa. (Amina Xu)