Masani game da huldar kasa da kasa dan kasar Senegal Amadou Diop, ya ce kasar Sin ta gabatarwa kasashen nahiyar Afirka, da ma sauran sassan duniya kyakkyawan misali bisa adalci, a fannin hadin gwiwa da cimma moriyar juna.
Diop ya bayyana hakan ne, yayin wata tattaunawa a baya bayan nan da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, inda ya ce sabanin irin ka’idoji da sharuddan da wasu kasashe, ko hukumomin kasa da kasa ke gindayawa kasashen na Afirka, kasar Sin na kokarin cimma nasarorin hadin gwiwa ne karkashin salo na cimma moriyar juna, gwargwadon manyan bukatun kasashen na Afirka.
Kaza lika a cewar sa, Sin na taimakawa nahiyar Afirka, da nufin bunkasa muhimman ayyukan bunkasa tattalin arziki da zamantakewa, da raya al’adu, kamar ginin manyan hanyoyin mota, da asibitoci, da makarantu, da gadoji.
Bugu da kari, Diop ya tabbatar da cewa, hadin gwiwa tsakanin Sin da nahiyar Afirka, na mayar da hankali ne ga samar da ci gaba, inda Sin din ta taimakawa sassan nahiyar wajen gina dinbin ababen more rayuwa. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp