Cikin shekaru 20 da suka gabata kawo yanzu, kasar Sin ta himmatu wajen gina tsarin tattalin arziki mai kiyaye muhallin halittu, da ingiza sabon karfi da fifikon bunkasa kai, karkashin tsarin kare muhalli bisa matsayin koli.
Wani rahoton hadin gwiwa na cibiyar kwararru ta Xinhua dake karkashin kamfanin dillancin labarai na kasar Sin Xinhua, da cibiyar bincike game da tunanin shugaba Xi Jinping dangane da wayewar kai ta fuskar kare muhallin halittu ne ya bayyana hakan.
Rahoton da aka fitar a yau Lahadi, mai taken “Kyakkyawan ruwa, da tsaunuka masu ban sha’awa, da Sin da duniya masu kayatarwa: Yanayin wayewar kan Sin ta fuskar kare muhallin halittu, da ayyukan da kasar ke gudanarwa a fannin, da yadda take zaburar da duniya,” ya fayyace turbar samar da ci gaba, dake sauya damammaki da ake da su a fannin kare muhallin halittu zuwa tarin gajiya, ta hanyar kare yanayin muhallin halittu, da tabbatar da gudummawar wuraren, da tsarin cin gajiya daga wuraren masu matukar daraja.
Kazalika, rahoton ya ce, Sin ta kuma tsara wata turba, ta bunkasa tattalin arziki ta hanyar cimma gajiya daga damammakin muhallin halittu, ciki har da noma ta amfani da albarkatu, da yawon shakatawa da masana’antu masu nasaba da hakan. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp