Mataimakiyar ministan kasuwanci na kasar Sin Guo Tingting ta bayyana cewa, an samu karuwar sabbin kamfanonin waje da suka zuba jari a watanni shida na farkon wannan shekara a kasar Sin.
Jami’ar ta shaidawa taron manema labarai Larabar nan cewa, a cikin watanni shida na farkon shekarar nan, an samu kafuwar wasu sabbin kamfanonin ketare guda dubu 24 a cikin kasar Sin, karuwar kashi 35.7 cikin 100 kan na shekarar da ta gabata.
Guo ta ce, an samu daidaituwar yadda ake zuba jarin waje a kasar a wannan lokacin. (Mai fassara: Ibrahim)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp