Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana a yau 28 ga wata cewa, tallafawa ci gaban Afirka nauyi ne da ya rataya a wuyan kasashen duniya. Kuma kasar Sin tana maraba da sauran kasashen duniya da su kara zuba jari a nahiyar Afirka kamar yadda kasar Sin take yi, kana a shirye take ta yi aiki tare da kasashen duniya wajen sa kaimi ga bunkasuwar Afirka tare da samar da ci gaba da wadata da amfanar jama’a Afirka tare.
A kwanakin baya, Hannah Ryder, wata kwararriya a fannin tattalin arziki ta kasar Kenya, kuma tsohuwar mataimakiyar daraktar shirin raya kasashe na MDD, ta bayyana a cikin wata hira cewa, ba a bukatar kasashen Afirka su sauya manufofinsu ala tilas kan yin hadin gwiwa da kasar Sin. Ana gudanar da hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka ne bisa ga bukatun kasashen Afirka, kuma wannan shi ne hali na musamman dake tattare da hadin gwiwar bangarorin biyu, wanda ya sa kasashen yammacin duniya da sauran abokan hadin kai suke kara yin la’akari da bukatun Afirka, da kulla alaka mai zaman daidai wa daida da Afirka.
Da yake amsa tambayoyin manema labaru da suka shafi batun, Lin Jian ya ce, tun fil azal, moriyar jama’ar Sin da Afirka ita ce tushen hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka, kuma kasar Sin ta himmatu wajen sa kaimi ga bunkasuwar Afirka tare da ci gaban kasar Sin, da sa kaimi ga zamanantar da Afirka ta hanyar zamanantarwa irin ta kasar Sin. Hakazalika, a ko da yaushe kasar Sin na nacewa ga tabbatar jin dadin jama’ar Afirka, da ma bukatunsu, da mutunta juna, da tabbatar da daidaito tsakanin juna, kuma Sin ba ta taba dora son ranta a kan wasu ba, balle ta nemi moriyar kanta ita kadai. (Yahaya)