Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta ce kasar na maraba da ziyarar sakataren harkokin wajen Amurka Anthony Blinken, kuma bangarorin biyu na tuntubar juna kan shirye-shiryen ziyarar.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin, Wang Wenbin ne ya bayyana haka, yayin taron manema labarai na yau Talata.
Rahotanni daga kafafen yada labaran Amurka na cewa, sakataren harkokin wajen kasar, Anthony Blinken, zai ziyarci kasar Sin a ranar 5 ga watan Fabreru, domin ganawa da takwaransa na kasar Qin Gang.
Wang Wenbin ya ce, kasar Sin ta kasance mai daukar dangantakarta da Amurka tare da raya ta bisa ka’idoji 3 da suka hada da mutunta juna, da yin zaman tare cikin lumana, da kuma samun moriyar juna, kamar yadda shugaba Xi Jinping ya gabatar. Ya kuma yi fatan Amurka za ta yi wa Sin kyakkyawar fahimta da nacewa ga tattaunawa maimakon fito na fito, da moriyar juna maimakon danne wani bangare domin samun nasara, da hada hannu da kasar Sin da kuma aiwatar da muhimman batutuwan da shugabannin biyu suka cimma, tare da mayar da dangantakar kasashen biyu bisa turbar ci gaba cikin aminci.(Fa’iza)